28/05/2026
MOUNT NYIRAGONGO – VOLCANO MAFI HAƊARI A AFRIKA
Shin ka san akwai wani volcano a Afirka da ke ɗauke da ɗaya daga cikin mafi girman tafkunan lava a duniya?
Yana a gabashin DR Congo 🇨🇩, kusa da birnin Goma.
- Tsayinsa ya kai kusan 3,470 meters
- Active volcano ne
- Yana da babban lava lake a saman sa
Me Ya Sa Ya Ke Da Haɗari?
Lava ɗin Nyiragongo yana da ruwa sosai idan aka kwatanta da na wasu volcanoes.
Saboda haka:
- Yana gudu cikin sauri
- Yana iya isa garuruwa cikin ɗan lokaci
⚠️ Babban Eruption:
A shekarar 2002, lava ta shiga cikin birnin Goma, ta lalata gidaje da hanyoyi.
MUHIMMANCI:
- Binciken kimiyya
- Yawon buɗe ido
- Fahimtar yadda volcanoes ke aiki
Masana suna ɗaukar Mount Nyiragongo a matsayin ɗaya daga cikin volcanoes mafi haɗari a duniya!
TAMBAYA
Kana ganin me ya sa mutane har yanzu suke rayuwa kusa da volcano duk da haɗarinsa?
Follow: GeoHausa Hub domin ƙarin ilimin Geography!
26/05/2026
KWATANTA MANYAN TSAUNUKAN AFRIKA
Mun koyi game da manyan tsaunuka a Afirka. Yanzu mu ga yadda suke kwatantuwa da juna!
Kwatancen Manyan Tsaunuka na Afirka.
DUTSE ƘASA TSAYI
Mount Kilimanjaro Tanzania 🇹🇿 5,895 m
Mount Kenya Kenya 🇰🇪 5,199 m
Rwenzori
(Mount Stanley) Uganda/DR Congo
🇺🇬🇨🇩. 5,109 m
Mount Cameroon Cameroon 🇨🇲 4,040m
Mount Toubkal (Atlas) Morocco 🇲🇦 4,167m
Drakensberg (Thabana
Ntlenyana) Lesotho 🇱🇸 3,482m
WANENE YA FI?
Mafi tsawo: Mount Kilimanjaro (5,895 m)
Mafi shaharar ƙanƙara: Kilimanjaro & Rwenzori
Volcano mafi shahara: Mount Cameroon
Mafi kyawun yanayi: Drakensberg
Mafi kusa da Sahara: Atlas Mountains
Mafi ban mamaki: Rwenzori (Mountains of the Moon)
Kilimanjaro shi ne mafi tsawon dutse mai zaman kansa (free-standing mountain) a duniya.
Rwenzori yana da glaciers duk da yana kusa da Equator.
Mount Cameroon yana daga cikin volcanoes masu aiki a Afirka.
Atlas Mountains suna taimakawa rage tasirin Sahara a wasu yankuna.
25/05/2026
🏔️ DRAKENSBERG – MAFI KYAWUN TSAUNUKA A KUDANCIN AFRIKA
Shin ka san akwai wasu tsaunuka a Afirka da ake kira "Dragon Mountains" (Tsaunukan Maciji Mai Fuka-fuki)?
Suna tsakanin:
South Africa 🇿🇦 Da Lesotho 🇱🇸
- Mafi shahararrun tsaunuka a Kudancin Afirka
- Tsawonsu ya haura kilomita 1,000
- Suna da kololuwa masu tsayi da kwazazzabai masu ban mamaki
🏔️ Mafi Tsawon Kololuwa:
Thabana Ntlenyana
- Tsayinsa: kusan 3,482 meters.
- Ciyayi masu kore
- Ruwa da rafuka masu yawa
- Dazuzzuka
- Dabbobin jeji
- Tushen ruwa ga miliyoyin mutane
- Yawon buɗe ido
- Hawan dutse
- Kula da muhalli
Akwai tsoffin zane-zanen dutse (rock paintings) da mutanen San s**a bari a cikin Drakensberg tun dubban shekaru da s**a wuce!
TAMBAYA
Idan za ka ziyarci tsauni ɗaya a Afirka, shin za ka zaɓi Kilimanjaro ko Drakensberg?
Follow: GeoHausa Hub domin ƙarin Geography!
24/05/2026
🌙 RWENZORI MOUNTAINS – TSAUNUKAN WATA
Shin ka san akwai tsaunuka a Afirka da ake kira "Mountains of the Moon"?
Suna tsakanin:
- Uganda 🇺🇬 Da DR Congo 🇨🇩
- Daya daga cikin manyan tsaunuka a Afirka
- Suna kusa da Equator
- Amma suna da ƙanƙara da glaciers .
🏔️ Mafi Tsawon Kololuwa Mount Stanley
- Tsayinsa: kusan 5,109 meters, Duk da suna kusa da Equator.
- Ana samun snow
- Ana samun glaciers
- Yanayin sanyi sosai a saman tsaunukan
- Dazuzzuka masu duhu
- Tsirrai na musamman
- Dabbobi iri-iri
Tsoffin masu bincike sun yi imanin cewa Rwenzori Mountains na daga cikin tushen Kogin Nile!
TAMBAYA
Kana ganin me yasa ake kiransu "Mountains of the Moon"? 🌙
Follow: GeoHausa Hub domin ƙarin ilimin Geography!
22/05/2026
🏔️ ATLAS MOUNTAINS – KATANGA TSAKANIN SAHARA DA AREWA 🌍
Shin ka san akwai wasu manyan tsaunuka da suke taimakawa wajen rage yaduwar hamadar Sahara?
Suna cikin:
- Morocco 🇲🇦
- Algeria 🇩🇿
- Tunisia 🇹🇳
- Daya daga cikin manyan mountain ranges a Afirka
- Suna raba Sahara da yankin Mediterranean
- Tsawonsu ya haura dubban kilometer.
-Ya Taimakawa samun ruwan sama
- Ya Rage yaduwar hamada
- Ya Samar da ruwa ga gonaki
- Tourism & hiking
Akwai:
- Dazuzzuka
- Dabbobi masu yawa
- Kankara
Mafi tsawon dutse a Atlas Mountains shine Mount Toubkal (4,167 m) a Morocco!
TAMBAYA
Kana ganin me yasa tsaunuka suke hana hamada yaduwa?
Follow: GeoHausa Hub domin ƙarin bayanan Geography mai ban sha’awa!
21/05/2026
🏔️ MOUNT KENYA – DUTSE MAI BAN SHA’AWA
Shin ka san akwai wani babban dutse a Afirka da yake da dazuzzuka, dabbobi, da ƙanƙara a lokaci guda?
Yana ƙasar Kenya 🇰🇪
- Dutse mafi tsawo na biyu a Afirka
- Tsayinsa ya kai kusan 5,199 meters
- Yana kusa da Equator
ABIN MANAKI
Duk da yana kusa da Equator, saman dutsen yana da:
- snow
- glaciers
MUHIMMANCI:
- Tushen ruwa 💧
- Tourism
- Muhalli ga dabbobi 🐘
- Noma a yankunan kusa
DABBOBIN YANKIN
- Giwaye 🐘
- Buffalo
- Birai 🐒
- Tsuntsaye masu yawa
Mount Kenya yana cikin wuraren UNESCO World Heritage Site! 🌍
TAMBAYA
Kana ganin me yasa manyan tsaunuka suke taimakawa wajen samar da ruwa?
Follow: GeoHausa Hub domin ƙarin Geography mai ban sha’awa!
21/05/2026
🏔️ MOUNT KILIMANJARO – GIANT OF AFRICA
Shin ka san mafi tsawon dutse a Afirka yana da ƙanƙara a samansa?
Yana ƙasar Tanzania 🇹🇿
- Mafi tsawon dutse a Afirka
- Tsayinsa ya kai kusan 5,895 meters
- Daya daga cikin manyan volcanoes a duniya
🌋 Volcano ne?
Eh! Kilimanjaro dormant volcano ne, ma’ana baya yin eruption yanzu amma volcano ne.
ABIN MANAKI:
Duk da yana Afirka mai zafi, saman dutsen yana da:
- snow
- ice glaciers.
MUHIMMANCI:
- Tourism
- Hawan dutse (mountain climbing)
- Muhalli da ruwa.
Dubban mutane daga duniya suna hawa Mount Kilimanjaro kowace shekara!
TAMBAYA
Kana ganin me yasa akwai snow a saman dutse duk da zafin Afirka?
Follow: GeoHausa Hub domin ƙarin Geography mai ban sha’awa!
19/05/2026
MANYAN TAFKUNA NA AFRIKA – Wanne ne mafi girma?
Mun koyi manyan tafkuna na Afirka… yanzu lokaci ne na kwatantawa!
Tafki Da Abin da ya fi shahara da shi.
Lake Victoria: Mafi girma a Afirka
Lake Tanganyika: Daya daga cikin mafi zurfi a duniya
Lake Malawi: Tafkin kifaye masu yawa
Lake Chad: Tafkin da yake raguwa
Lake Turkana: Tafki mafi girma a hamada
Lake Albert & Edward: Suna cikin tsarin River Nile.
Afirka tana da wasu daga cikin:
- mafi girman tafkuna
- mafi zurfi
- da mafi ban mamaki a duniya
TAMBAYA:
Wanne tafki ne ya fi baka mamaki?
1️⃣ Lake Victoria
2️⃣ Tanganyika
3️⃣ Malawi
4️⃣ Chad
5️⃣ Turkana
6️⃣ Albert & Edward
👇 Rubuta amsarka a comments!
Follow: GeoHausa Hub domin ƙarin bayanan Geography mai ban sha’awa!