Mallam Munzir Yusuf Ali-Sarkin Malaman Gaya

Mallam Munzir Yusuf Ali-Sarkin Malaman Gaya

Share

Munzir Yusuf Ali is the Sarkin Malaman Gaya, one of the emirates in Kano state.

He is the head of all Islamic scholars in the emirates and advice His Royal Highness on Islamic affairs.

05/01/2026

Bayan kammala Addu’o’in da muka gudanar na Saukar Al-Qur’ani Mai Girma guda 21, mun ci gaba da gudanar da Addu’o’i na musamman domin neman zaman lafiya, ci gaba da albarka ga ƙasarmu Najeriya, jiharmu Kano, da Maimartaba Sarkin Gaya da Kuma Masarautarmu, sannan da dukkan masoyanmu da al’ummar Musulmi baki ɗaya.
Haka nan, a wannan lokaci mai albarka, mun ƙara kebance addu’a ta musamman ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, shugaba nagari, mai kishin al’umma, kuma jagora mai hangen nesa. Mun roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da Ya shige masa gaba a dukkan al’amuransa, Ya ƙara masa hikima, juriyar shugabanci, da ikon gudanar da al’amuran jama’a bisa gaskiya da adalci.
Mun kuma yi masa addu’ar cewa Allah Ya ƙara taimakonsa, Ya ƙarfafa masa guiwa, Ya tsare shi daga sharrin ma hassada tare da roƙon Allah Ya maimaita masa wannan kujerar, domin mu ci gaba da amfana da nagartaccen shugabancinsa, ayyukansa na alheri, da manufofinsa na bunƙasa rayuwar al’umma wanda Mu Yan Gaya ganau ne.
Muna roƙon Allah Ya sanya mulkinsa ya zamo na albarka, ya kasance ginshiƙin zaman lafiya, ci gaba da haɗin kai, kuma ya bar tarihi na alheri da za a riƙa tunawa da shi har bayan mulkinsa.
Allah Ya kare Kano, Ya ɗaukaka shugabanninmu nagari, Ya kuma sanya mu a cikin masu yi wa ƙasa addu’a da aiki na gaskiya. Ameen.

Sarkin Malaman Gaya.

02/01/2026

Assalamu Alaikum 🔥🔥🔥

Idan Allah Ya kaimu gobenJuma’a, wadda ta yi daidai da 02 ga Janairu, 2026, da Misalin Karfe 10:00 zuwa bayan La'asar za mu gudanar da addu’o’in shiga sabuwar shekara, k**ar yadda magabatanmu s**a saba yi.
A cikin shirin:

-Za a yi saukar Alƙur’ani guda 21
-Za a yi li'ilafi kafa 12,000 da niyyar kariya
-Za a karanta “Laqad jā’akum” da adadin kwanakin shekara, da niyyar Allah Ya sa mu kai ƙarshenta cikin lafiya da aminci
-Za a karanta “Yā Laṭīfu Yā Razzāqu” da niyyar mutanen da muke hulɗa da su masu sana’a, ko aiki domin Allah Ya ƙara musu buɗi da daukaka wanda zamu fadi sunansu a gurin k**ar Yadda muka saba yi musu Addua

A kowace sauka, za a karanta Suratu Yāsīn sau 41, da niyyar zaman lafiya da kwanciyar hankali da budi.

Za'a gudanar da wannan addu'oi a a unguwar Tudun Maliki Kano, Gidan Sarkin Malaman Gaya Sheikh Dr. Yusuf Ali.

Muna roƙon Allah Ya ba mu lafiya da zaman lafiya, Ya ba mu ikon aiwatar da wannan ibada cikin tsarkakkiyar niyya, Ya cire riya daga zukatanmu, Ya kuma karɓa daga gare mu.
Āmīn.

Daga Fadar Sarkin Malaman Gaya, Malam Munzir Yusuf

02/01/2026

Assalamu Alaikum

Idan Allah Ya kaimu gobenJuma’a, wadda ta yi daidai da 02 ga Janairu, 2026, da Misalin Karfe 10:00 zuwa bayan La'asar za mu gudanar da addu’o’in shiga sabuwar shekara, k**ar yadda magabatanmu s**a saba yi.
A cikin shirin:

-Za a yi saukar Alƙur’ani guda 21
-Za a yi li'ilafi kafa 12,000 da niyyar kariya
-Za a karanta “Laqad jā’akum” da adadin kwanakin shekara, da niyyar Allah Ya sa mu kai ƙarshenta cikin lafiya da aminci
-Za a karanta “Yā Laṭīfu Yā Razzāqu” da niyyar mutanen da muke hulɗa da su masu sana’a, ko aiki domin Allah Ya ƙara musu buɗi da daukaka wanda zamu fadi sunansu a gurin k**ar Yadda muka saba yi musu Addua

A kowace sauka, za a karanta Suratu Yāsīn sau 41, da niyyar zaman lafiya da kwanciyar hankali da budi.

Za'a gudanar da wannan addu'oi a a unguwar Tudun Maliki Kano, Gidan Sarkin Malaman Gaya Sheikh Dr. Yusuf Ali.

Muna roƙon Allah Ya ba mu lafiya da zaman lafiya, Ya ba mu ikon aiwatar da wannan ibada cikin tsarkakkiyar niyya, Ya cire riya daga zukatanmu, Ya kuma karɓa daga gare mu.
Āmīn.

Daga Fadar Sarkin Malaman Gaya Malam Mallam Munzir Yusuf Ali-Sarkin Malaman Gaya

08/12/2025

Sarkin Malaman Gaya Malam Munzir Sheikh Dr. Yusuf Ali Daga Wajen Ɗaurin Auren Ballah Family.

04/12/2025
07/08/2025

Kano tana kuka, muna kallo”

A yau, cikin manyan tituna da ƙananan unguwanni na Kano, rayukan bayin Allah suna salwanta saboda abin da ya zama ruwan dare — kwacen waya. An fi kai farmakin matasa, da daddare ko da rana tsaka. Wani lokaci, saboda waya ta ₦20,000, rayuwa mai daraja sai ta zama ta Salwanta.

’Yan daba sun mamaye birni. Unguwanni da dama sun koma k**ar filin yaki. Fadan ‘daba yana haddasa kashe juna, fasa shaguna, da haddasa firgici ga jama’a. Iyaye sun daina barin ‘ya’yansu su fita da yamma saboda tsoro.

Ina gwamnati? Ina masu iko? Ina jami’an tsaro?

Allah Ya sakawa Maigirma Gwamanan Kano da Alkhairi Abba Kabir Yusuf
Yana Kokarinsa sosai wajan tabbatar da jahar kano ta samu tsaro, yana bin hanyoyi da yawa sosai dan tabbatar da hakan ga jami’an tsaro tare da sa Malamai su dinga Addua sosai kan zaman lafiya.

Amma mu sani ba gwamnati kadai za a Sawa ido ba ya k**ata muma muyi namu

Ina da Shawarwari Maigirma Gwamna

1 A ɗora Alhakin tsaro akan Sarakuna, Hakimai da Jagororin unguwanni. Su rika bayar da rahoto kai tsaye.

2. A kafa wani layin waya na gaggawa da jama'a zasu iya kira idan akwai barazana.

3. A buɗe cibiyoyin gyaran hali da koyon sana’a ga matasa. Yawancin waɗanda s**a shiga kwacen waya da daba suna cikin yunwa da jahilci.

4 A rika gudanar da Adduoi tare da Saukar Alkurani a duk wasu unguwanni da muke su a kano akan Allah Ya kawo Zaman Lafiya sai saukar ta zama karkashin jagorancin Mai Unguwa, Kuma Yan unguwa Su bada Hadin kai

5. A saka matasan da s**a tuba cikin Harkar daba da shaye a bijilanti na unguwa

6 A bude gidajan Mari

7. A kafa kwamitin haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da masu unguwanni domin gaggauta yanke hukunci.

8. A ɗora hukunci mai tsauri akan duk wanda aka k**a da kwacen waya ko fadan daba.

9. A wayar da kan iyaye akan kula da tarbiyyar ‘ya’yansu — da yawa daga masu laifi suna cikin gida ba tare da tarbiyya ba.

Allah Ka bamu Lafiya da Zaman Lafiya Amin

Sarkin Malaman Gaya.

25/07/2025

Harafin sa suna cika zuciya da tsarki,
Duk mai karantawa yana samu natsuwa.
Kowa ya kalli saƙonsa da hankali,
Zai ji k**ar Allah na magana da shi kai tsaye.

Waraka ne ga marasa lafiya,
Kariya ne ga masu tsoron shaiɗan.
Mai ɗauke da hikima, da sirri na gaskiya,
Duk wanda ya karanta, albarka ya samu har abada.

Yabo gareka Ya Al-Qur’ani mai daraja,
Mun ɗauke ka da zuciya, ba da wasa ba.
Za mu karanta ka da dare da rana,
Har sai ka zamo shaida mana gaban Allah.

Allah Ka bamu Albarkacin Alqur ani Maigirma, Allah Ya qara Mana Kusanci da Annabi Salallahu alaihi Wasallam.

Juma'at Khareem.

S.M.G

18/05/2025

HIKIMAR ALLAH!

Za ka iya ganin yaro na wasa da abin da zai cutar da shi, idan ka kwace, ya yi kuka, ko kuma ba shi da lafiya, idan ka ba shi magani, sai ya yi kuka. A ilmin yaron yana ganin abin wasan maslaha ne, a na ka ilmin kana ganin cutuwa ne, yana ganin magani cutuwa ne, kai kana ganin maslaha ne. Wannan tazarar ilminka da na yaro kenan, to ka duba tazarar ilminka da na ALLAH! Idan ALLAH Ya ba ka ko ya karbe, to ka kyautata masa zaton alheri Yake nufi da kai, wanda ilminka bai kai ya sani ba, k**ar yadda ilmin yaro bai kai ya san abin da zai cutar ko amfane shi ba.

S.M.G.

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Telephone

Website

Address

No 348/349 Tudun Maliki
Kano
700233