Ahsan AL-hadith

Ahsan AL-hadith

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Ahsan AL-hadith, Education Website, .

Ahsan AL-hadith – Shafi ne da ke yada ilimi daga malamai, tare da bidiyo da karatuttuka kan addinin Musulunci bisa koyarwar Annabi (SAW), don ƙara fahimta da kusanci da addini.

20/06/2025

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ ‎وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ كَمَا صَلَّيْتَ ‎عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ ‎إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ ‎اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ ‎وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ كَمَا بَارَكْتَ ‎عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ ‎إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ.

20/06/2025

🌙 Falalar Ranar Juma’a 🕌

Ranar Juma’a rana ce mai albarka, wadda ta fi kowace rana a cikin mako daraja.

📖 Manzon Allah (SAW) ya ce:
"Mafi falala daga ranakunku ita ce Juma’a. A cikinta ne aka halicci Annabi Adam, kuma a cikinta ne za a busa ƙaho (ƙiyama)." – (Abu Dawud)

🕋 Abubuwan da ake so a yi a wannan rana: ✅ Yin wanka (ghusl)
✅ Karanta Suratul Kahf
✅ Yawaita Salatin Annabi (SAW)
✅ Neman gafara da addu’o’in alheri
✅ Zuwa sallar Juma’a da wuri

🕯️ Ka amfana da wannan rana mai albarka, domin cike take da rahama da lada mai yawa!





’a
’a

05/06/2025
03/06/2025

03/06/2025

03/06/2025

YAWAN MUTANE ARZIƘI NE AMMA DA SHARAƊI.

Babu arziƙin da ya kai yawan mutane idan an iya sarrafa su, haka babu talaucin da ya kai yawan mutane idan an bar su kara zube.

Wasu ƙasashe suna da yawa amma suna da arziƙi wasu ƙasashan suna da yawa amma suna cikin talauci.

Ga jerin ƙasashe 10 da s**a fi yawan jama'a a duniya (dangane da bayanan kididdiga na baya-bayan nan – 2024):

🏳️‍🌍 Ƙasashe 10 da s**a fi yawan jama'a:

1 India ~1.43 biliyan

2 China ~1.41 biliyan

3 United States ~340 miliyan

4 Indonesia ~280 miliyan

5 Pakistan ~240 miliyan

6 Nigeria ~225 miliyan

7 Brazil ~215 miliyan

8 Bangladesh ~175 miliyan

9 Russia ~145 miliyan

10 Mexico ~130 miliyan

Lura: India ta wuce China a yawan jama'a tun daga shekarar 2023, bisa ga rahotannin Majalisar Ɗinkin Duniya (UN).

Ilmi da Sana'a da tarbiyya, da kishin ƙasa.

03/06/2025

MATSALOLIN MU A FILI SUKE

1. Muna aure ba tare da soyyayya ba.

2. Muna haihuwa ba tare da yin tarbiyya ba.

3. Muna salla ba tare da tsaron Allah ba.

4. Muna koyan ilmi ba tare da aiki ba.

5. Muna magana ba tare da gaskiya ba.

6. Muna daukan alƙawari ba tare da cikawa ba.

7. Muna karɓar amana ba tare da kulawa ba.

8. Muna son kuɗi ba tare da Sana'a ba.

9. Muna son Annabi (SAW) ba tare da bin koyarwar sa ba.

10. Muna son Aljannah ba tare da aiki ba.

11. Muna son a amsa mana addu'a ba tare da cin halal ba.

12. Gamu da bala'in son duniya da ƙin mutuwa.

Mafita kawai mu tuba mu gyara, muce Allah mun tuba ka yafe mu.

Want your school to be the top-listed School/college?

Website