07/06/2026
Yau Lahadi 21 Dhul-Hajj 1447AH, shugaban rundunar agaji na kasa da kasa Alhaji Isa Waziri Muhammad Gombe tare da mataimakinsa na biyu Alhaji Musa Adamu GG, sun kai ziyara ta musamman a gidan Sheikh Jingir da ke Jos.
Sheikh Jingir ya tarbesu da hannu biyu cikin farin ciki, kamar yadda ya saba yi.
06/06/2026
Aikin Alkhairi Yana yaduwa kamar yadda aikin sharri ke yaduwa , ka dage ka aikata alkhairi komin karancin sa Kuma ka dage ka guje ma sharri komin dadin sa. Muhalli biyu mutun baya da na ukkun su (wuta ko Aljannah) kayi tunani da kanka Ina zaka zaba. Allah ya datar damu.
06/06/2026
"لَا تَأْتِيكُمْ إِلَّا بَغْتَةً"
"Ba za ta zo muku ba sai kwatsam" ba zato ba tsammani 😭😭
06/06/2026
Big shout-out to my newest top fans! Umar Farukq Adam, Idris Umar Abba, Bello Iliya AJ, Ibrahim Sale, Adam Ibrahim YLere, Dan Asabe Dogon Yaro, Jabir Musa Uthman, Umat Bello Dangaladima, Musa Aliyu K Bura, Abdullahi Ndako Futminna, Shehu Umar, Abubakar Salahuddeen, Abubakar Rabiu Adoh Arac, Bashir Mshelia Abdullahi, Anas Prince Umar, Usama Aminu, Aliyu Muhammad Auwal, Salihu Jamilu Hamza, Is'haqa Jibrin, Alhaji Gentle, Abdullahi Haruna, Mr Tajuddeen Nuhu, Khalid Aliyu, Adamu Dalhatu Jos, Abdurrahim Abdullahi, Ibrahim Abubakar Abbarh, Isah Abdullahi Nakowa Gulu
06/06/2026
Wa'azi mai kyau shi ne wanda yake koyarwa, gyarawa, da kuma kusantar da mutane zuwa ga Allah cikin hikima, tausayi da kyakkyawar magana.
Ministan musabaqa Aminullah journal
05/06/2026
Muna kaunar Sheikh Jingir ne saboda irin kyawawan halaye da Allah Ya kebance shi da su. Yana da jajircewa wajen kare akidar Ahlus Sunnah, tare da fadin gaskiya ba tare da tsoro ko son rai ba. Haka kuma yana da hakuri, tawali'u, juriya da kuma kulawa da al'ummarsa.
Shehin Malamin ya sadaukar da rayuwarsa wajen yada ilimi, tarbiyya da kira zuwa ga tafarkin Al-Qur'ani da Sunnah. Duk da yawan kalubalen da yake fuskanta, bai taba gajiyawa ko ja da baya ba wajen yi wa addini hidima.
Wadannan halaye masu kyau ne s**a sanya Sheikh Jingir ya zama abin kauna, girmamawa da koyi ga miliyoyin musulmi a Najeriya da ma kasashen duniya. Allah Ya kare shi, Ya kara masa lafiya da albarka. Ameen.
05/06/2026
Pre Khuduba
Sheikh Yusuf sambo Rigacikum
Ahlul Qur'an TV Ɗalibin Sunnah Aminullah journal Ministan musabaqa