Hausa AI Academy

Hausa AI Academy

Share

> � Hausa AI Academy — Your Hub for AI & Modern Tech Learning in Hausa!

� Muna koyarwa akan yadda

17/12/2025
10/08/2025

Cikakken sunana Ibrahim Zubairu Baba, dan asalin Arewa amma na tashi a cikin birnin Legas. Na kammala digiri na farko a fannin Kimiyyar Kwamfuta daga Jami’ar Legas, sannan na yi MBA a Dangote Business School. Yanzu haka ina ci gaba da karatun Masters a Management Information Technology.

Tun ina ƙarami, zuciyata na cike da sha’awar fasaha — ina lalubo na’urori, in warware su, in fahimci yadda suke aiki. Wannan sha’awa ce da ta ja hankalina har na gina aikina gaba ɗaya a kai.

Yayin da na ke rayuwa a Legas, na ga yadda fasaha ke bunƙasa. Amma duk lokacin da na dawo Arewa, sai na tarar da tarin matasa da ƙwarewa amma ba tare da damar amfani da ita ba. Abin da ya fi daga min hankali shi ne yadda harshe ya zama babban shamaki: Turanci ya mamaye duniyar ilimi da fasaha, alhali har yanzu akwai miliyoyin mutanenmu da ba sa iya magana da shi sosai.

Wannan ne ya sa na kafa Skill Arewa (wanda aka fi sani da The North Tech Hub) tare da wasu abokaina. Manufarmu ita ce kawo ilimin zamani cikin harshen da mutane s**a fi fahimta — Hausa. Na gano cewa idan aka koyar da fasaha a cikin harshen gida, shingen da ke hana mutane shiga zai karye, ƙwarin gwiwa kuma zai ƙaru.

A karkashin Skill Arewa da Malamiromba Ltd, muna shirya horo, ƙirƙirar ƙunshe-ƙunshe, da gina al’umma inda kowani matashi ko dattijo, mai digiri ko mara shi ,zai iya koyon fasaha, fahimtar AI, ChatGPT, da sauran sabbin kirkire-kirkire. Muna tabbatar da cewa fasaha ta zama ta kowa, ba ta wani rukuni kaɗai ba.

A gare ni, wannan ba kawai buri ba ne — shi ne aikina, shi ne dalilin tashi na kowacce safiya.Ina son ganin matasanmu suna ƙirƙira, suna jagoranci, suna alfahari da harshe da al’adunsu a duniyar fasaha.

05/08/2025

Yadda zaka duba Numban wayanka na Airtel cikin sauki

05/08/2025

Yadda zaka ragewa wayanka shan Data ta hanya mafi sauƙi

03/08/2025

🤖🧠 AI vs Hankalin Ɗan Adam – Za a iya maye gurbin ɗan Adam da na’ura?

Photos from Hausa AI Academy's post 30/07/2025

Domin koyon irin wa'ennnan hotunan follow us

25/07/2025

🧠 YADDA ZAKA YI AMFANI DA GOOGLE TRANSLATE CIKIN SAUKI! 🌐📲

Shin kana son fassara rubutu daga Turanci zuwa Hausa ko daga Hausa zuwa wata harshe cikin sauki? 🗣️📝

To ka tsaya ka kalli wannan bidiyo domin zai nuna maka: ✅ Yadda zaka sauke ko shiga Google Translate
✅ Yadda zaka fassara rubutu kai tsaye
✅ Yadda zaka fassara ta hanyar magana ko hoton rubutu
✅ Kuma yadda zaka yi amfani da shi koda baka da internet!

📌 Wannan bidiyon na musamman yana taimakawa dalibai, malamai, masu kasuwanci da duk wanda ke bukatar fassara cikin gaggawa!

🖥️ Kalli bidiyon yanzu a shafinmu 👉 Hausa AI Academy
📢 Kada ka manta ka like, comment, da share domin wasu su amfana!

24/07/2025

"Yadda Zaka Hada CV da Cover Letter Cikin Minti 2 — FREE da AI!"
Kalli wannan bidiyo domin koyon yadda zaka tsara professional CV da cover letter cikin sauki ta amfani da ChatGPT da sauran fasahohin zamani — duk daga wayarka kawai!

✅ Babu bukatar kudi
✅ Yana da sauki sosai
✅ Yana da amfani ga masu neman aiki da dalibai
✅ Ana yi cikin mintuna kadan!

⏳ Kada ka bari a baka labari — koyi yanzu ka amfani da damar AI!
📲

Want your school to be the top-listed School/college in Maiduguri?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Website

Address

Maiduguri