Imam Muniru Adamu Koza

Imam Muniru Adamu Koza

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Imam Muniru Adamu Koza, Tutor/Teacher, Abuja.

wannan page an bude shi domin yada tatacciyar koyarwar addinin musulunci bisa fahimtar magabata nagari da kuma bada kariya daga dukkan masu yi masa batanci da shigar masa da abubuwan da basa cikinsa.

26/06/2026

BAMU GOYON BAYAN TAUYEWA KOWA HAQQINSA A QASAR NAN.

Naga wasu videos dake yawo a social media daga jiya zuwa yau, videos din kamar an daukesu ne a wata unguwa a Kano wadda ke nuna wasu jama'a (ina zaton yan shi'ah ne) sun fito kan wani uzurinsu na qashin kai, wanda ba na zaton doka zata haramta musu yin sa (matuqar babu barazanar tsaro a cikinsa).

Amma sai ga wasu matasa da nake zaton yan tada-zaune-tsaye ne koma watakila yan shaye-shaye (domin bana zaton mai hankali da tunani ko mai alaqa da wata fahimtar addini zai yi abinda s**a yi) sun fito suna jifar wadancan mutane da duwatsu har na ji wata murya daga gefe na cewa "BA ZAKU DAUKO MAKAMI BA?" (ko wani zance kamar haka)

In dai wannan video gaskiya ne ba editing ko AI ba (wanda binciken hakan ya rataya ne a wuyan hukumomi) to muna bada shawara ga jami'an tsaro da gaggawa suyi bincike tareda gaggauta kamawa da hukunta wadanda s**ayi wannan laifi domin daqile maimaituwar hakan nan gaba ko yaduwarshi zuwa wasu sassan qasar nan.

Barin hakan na faruwa zai qara dagula mana tsaron qasar nan wanda daman yana cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai
Na san kowa ya san illar da barin hakan ya cigaba da faruwa zata janyo mana a qasarmu mai albarka.

✍️Imam Munir Adam Koza
Shugaban Katsina Scholars Forum for Community Advancement (Zauren malaman Katsina domin cigaban al'umma)
منتدى علماء كشنه، لتقدم المجتمع

25/06/2026

RANAR ASHURA TSAKANIN HAQIQA DA SIYASAR RAWAFIDH DA NAWASIB

Yau ne 10 ga Muharram, ranar da aka fi sani da ranar Ashura, rana ce mai shu'umanci ga musulmi kuma mai fuska biyu
Akwai ibadar Azumi a cikinta wadda ya inganta daga SHUGABA ALAIHIS SALATU WAS SALAMU
Akwai kuma tunawa da mafi girman musiba da ta afkawa musulunci daga bayin duniya da mulki wadanda s**a sayar da addininsu da daukakarsu saboda nemanta, sune WASU SASHEN BANU UMAYYA (BA DUKA BA) ALLAH YA QARA NESANTASU DA RAHAMARSA, Na kisan SHUGABANMU DAN SHUGABANMU JIKAN SHUGABAN HALITTA WATO AL'IMAMUL HUSAINI ALAIHIS SALAMU.
Mu kula da kyau, Akwai abubuwa 2 a wannan ranar tabbatattu, sune

Abinda aka ruwaito a Sunna na azumi da yalwatawa iyali da muke ambata da cika-ciki (duk da wasu malamai na ganin rashin ingancin hadisan babin)

Sai kuma abinda ya afku na kisan IYALAN GIDAN SHUGABA SALLAL LAHU ALAIHI WA ALIHI WA SALLAMA

Sai kuma abu na uku da ya shigo ya hargitsa wadancan tabbatattun abubuwan, wato rigimar siyasar Rawafidh da Nawasib (ba zan ce shi'ah da Sunna ba) sai s**a fara canja wadancan tabbatattun abubuwa ta hanyar yarfen siyasar dake tsakaninsu

Ni a mahangata, ya kamata ace

~Abinda aka ruwaitoshi a Sunna na ayyukan ranar Ashura, mu riqe mu aikata mu nemi yardar Allah cikin aikatashi, in zamu musanta wani abu daga cikinsa to mu musantashi bisa doron dalili na ilmi kamar muce bamu yarda da cika-ciki ba saboda hadisansa ba su inganta ba misali, amma mu bar wanda yake ganin sun inganta ya aikata ba tareda jingina masa qiyayyar AHLUL BAITI BA, ko zargin shi da cewa yana yi ne don murnar ta'addancin da la'annu s**a yiwa mafi tsarkin halittar Allah a bayan qasa a ranar a Karbala.

~Wanda jimami ya shagaltar dashi daga ayyukan ranar Ashura muyi masa uzuri cewa lallai munin abun ya isa ya mantar da mutum duk wani aiki da ba na farilla ba.

Mu dai matsayar mu ta Sufaye mabiya Dariqa shine
Mu a wurin mu kullum ma Ashura ce kuma kowane gari ma Karbala ne, dangane da damuwarmu da jimami da baqin cikin mu akan abinda aka yiwa AHLUL BAITI kamar yadda Al'imamul Busiri yake cewa
كل يوم وكل أرض لكربي
منهم كربلا وعاشوراء.

24/06/2026

صلى الله عليه وعلى وآله وسلم

18/06/2026

Karatun Zaure
Riyadhus Saliheen halqah ta 23

17/06/2026

Karatun Asshifa halqah ta 32
Zagaye na 2

17/06/2026
17/06/2026

Karatun Zaure
Riyadhus Saliheen halqah ta 22

16/06/2026

Maulidin wata-wata
Fassarar Daibatul Garrah halqah ta 7

15/06/2026

Karatun Asshifa
Halqah ta 31 zagaye na 2

13/06/2026

Tattaunawar wata mata da Imam Muniru Adamu Koza lokacin da mijinta zai qara aure

Want your school to be the top-listed School/college in Abuja?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Telephone

Website

Address


Abuja