Sheikh Ibrahim Muhammad Duguri
The only official page of Sheikh Ibrahim Muhammad Duguri, Chairman Ulama'u Council Of Jibwis FCT Abuja.
11/06/2026
Ziyarar Taya Murna da Fatan Alheri
Shugaban Majalisar Malamai ta FCT Abuja, Sheikh Ibrahim Muhammad Duguri (Wakilin Malaman Bauchi), ya jagoranci wata ziyarar taya murna da fatan alheri ga Mataimakinsa na daya, Dr. Yahuza Ishaq Muhammad Jama’are, bisa nada shi da aka yi a matsayin Provost na Federal College of Education, Jama’are, Jihar Bauchi.
A yayin ziyarar, Sheikh Ibrahim Muhammad Duguri ya bayyana farin cikinsa kan wannan muƙami da aka ba Dr. Yahuza, yana mai cewa nadin ya zo ne sakamakon ƙwarewa, jajircewa da kuma gudummawar da yake bayarwa wajen ci gaban ilimi da al’umma.
Ya kuma yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya ba shi ikon sauke nauyin wannan babban amanar cikin adalci, hikima da nasara, tare da sanya wannan muƙami ya zama alheri ga ilimi, ɗalibai da al’ummar ƙasa baki ɗaya.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Website
Address
Abuja