School for Qur'anic Memorization Training

School for Qur'anic Memorization Training

Share

خيركم من تعلم القرآن وعلمه

15/06/2026

🕌📖 ALHAMDULILLAH! AN KAMMALA TADRIBUL QUR'AN 📖🕌

SCHOOL FOR QUR'ANIC MEMORIZATION TRAINING.

Alhamdulillahi Rabbil 'Alamin, cikin ikon Allah Maɗaukakin Sarki an samu nasarar kammala shirin Tadribul Qur'an cikin nasara da kwanciyar hankali.

Muna miƙa godiya ta musamman ga malamai, ɗalibai, iyaye da dukkan waɗanda s**a bayar da gudunmawa wajen ganin wannan shiri ya gudana cikin nasara.

Allah Ya saka wa kowa da alkhairi, Ya sanya abin da aka koya ya zama hujja a gare mu ba hujja a kanmu ba, Ya ƙara mana fahimta da riƙo da Al-Qur'ani Mai Girma.

"Mafificin ku shi ne wanda ya koyi Al-Qur'ani kuma ya koyar da shi."

🤲 Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya albarkaci iliminmu, Ya sa Al-Qur'ani ya zama haske a zukatanmu.
✨ Tadrib ya ƙare, amma tafiyar koyon Al-Qur'ani ba ta ƙare ba.
📖🤍🕌 Abdurrashid M. Sh*tu Bashir Lawal fans

14/06/2026
14/06/2026

📢 SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!! 📢

Hadaddiyar Ƙungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) NHQ JOSReshen Unguwar Rimi Ta Yamma

Na farin cikin sanar da ɗaukacin al'ummar Musulmi cewa za a gudanar da Wa'azin Reshe kamar haka:

📅 Rana: yau Lahadi, 14/06/2026🕌 Wuri: Masallacin Gidan Malam Badamasi Mai Kifi⏰ Lokaci: 06:40 na yamma

🎙️ Shugaban Taro:Ustaz Bashir Lawal Adam(Director, SFQMT Abul Huffaz)Shugaban Majalisar Malamai, Reshen Unguwar Rimi Ta Yamma, JIBWIS NHQ JOS.

📖 Kaɗan daga cikin Malamai Masu Wa'azi:

Ustaz Bashir Lawal Adam (AbulHuffaz)

Ustaz Sulaiman Usama

Ustaz Surajo Zakariyya

Ustaz Umar Khamis

Ustaz Hassan Yusuf Nuhu

Da sauran manyan malamai.

🎤 Alarammomi Masu Jan Baƙi:

Hafeez Yakub Aliyu

Hafeez Zaradin Aminu

Hafeez Sadik Isah

Hafeez Abubakar Lawal Adam

Hafeez Ibrahim Umar Muhammad

Da sauransu.

📌 Muna kira ga dukkan 'yan uwa Musulmi da su halarta domin amfana da karatun addini, wa'azi, da nasihohi masu amfani.

Sanarwa daga:Kwamitin Yaɗa Labarai da Tsare-tsareJIBWIS NHQ JOS, Reshen Unguwar Rimi Ta Yamma.

🤲 Allah Ya ba mu ikon halarta, Ya sa mu amfana da abin da za a gabatar. Ameen Ya Rabbal Alameen.

Bashir Lawal School for Qur'anic Memorization Training Kwamitin Wa'azin Matasa

Photos from School for Qur'anic Memorization Training's post 13/06/2026

╔══════════════════════════════════════╗ 🌙🕌📖 𝐃𝐀𝐘 𝟖 – 𝐒𝐀𝐒𝐇𝐈𝐍 𝐀𝐒𝐀𝐁𝐀𝐑 𝐃𝐀 𝐋𝐀𝐇𝐀𝐃𝐈 | 𝐂𝐈𝐆𝐀𝐁𝐀 𝐃𝐀 𝐆𝐔𝐃𝐀𝐍𝐀𝐑 𝐃𝐀 𝐓𝐀𝐃𝐑𝐈𝐁𝐔𝐋 𝐐𝐔𝐑'𝐀𝐍 📖🕌🌙 ╚══════════════════════════════════════╝
🌿 𝐀𝐒𝐒𝐀𝐋𝐀𝐌𝐔 𝐀𝐋𝐀𝐈𝐊𝐔𝐌 𝐖𝐀𝐑𝐀𝐇𝐌𝐀𝐓𝐔𝐋𝐋𝐀𝐇𝐈 𝐖𝐀 𝐁𝐀𝐑𝐀𝐊𝐀𝐓𝐔𝐇𝐔 🌿

✨ Alhamdulillah, cikin ikon Allah Maɗaukakin Sarki, an shiga Rana ta Takwas (Day 8) na gudanar da Tadribul Qur'an ga ɗaliban Sashin Asabar da Lahadi na l,

𝐒𝐂𝐇𝐎𝐎𝐋 𝐅𝐎𝐑 𝐐𝐔𝐑'𝐀𝐍𝐈𝐂 𝐌𝐄𝐌𝐎𝐑𝐈𝐙𝐀𝐓𝐈𝐎𝐍 𝐓𝐑𝐀𝐈𝐍𝐈𝐍𝐆.

📖 A wannan rana, ɗalibai sun ci gaba da karatun Al-Qur'ani Mai Girma tare da gyaran tajwidi, inganta lafazi, da kuma ƙara fahimtar ƙa'idojin karatu yadda ya kamata.

👨‍🏫 Malamai suna ci gaba da ba da jagoranci da kulawa domin tabbatar da ingantaccen koyo da haddar Al-Qur'ani.

🤲 Muna gode wa Allah SWT bisa wannan ni'ima da kuma ci gaban da ake samu a kowace rana. Allah Ya sa wannan karatu ya zama sanadin samun yardarsa da rabauta a duniya da lahira.
💫 Allah Ya ƙara mana ilimi mai amfani, fahimta mai zurfi, da ikhlasi a cikin ayyukanmu. 🤍

━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━ 📍 𝐒𝐂𝐇𝐎𝐎𝐋 𝐅𝐎𝐑 𝐐𝐔𝐑'𝐀𝐍𝐈𝐂 𝐌𝐄𝐌𝐎𝐑𝐈𝐙𝐀𝐓𝐈𝐎𝐍 𝐓𝐑𝐀𝐈𝐍𝐈𝐍𝐆 📖 Tadribul Qur'an – Day 8 🗓️ Sashin Asabar da Lahadi ━━━━━━━━━━━━━━━━━━━━
#𝐓𝐚𝐝𝐫𝐢𝐛𝐮𝐥𝐐𝐮𝐫𝐚𝐧 #𝐃𝐚𝐲𝟖 #𝐒𝐐𝐌𝐓 #𝐐𝐮𝐫𝐚𝐧𝐢𝐜𝐄𝐝𝐮𝐜𝐚𝐭𝐢𝐨𝐧 #𝐒𝐚𝐬𝐡𝐢𝐧𝐀𝐬𝐚𝐛𝐚𝐫𝐃𝐚𝐋𝐚𝐡𝐚𝐝𝐢 #𝐊𝐡𝐚𝐢𝐫𝐮𝐥𝐔𝐦𝐦𝐚𝐡 #𝐐𝐮𝐫𝐚𝐧𝐌𝐞𝐦𝐨𝐫𝐢𝐳𝐚𝐭𝐢𝐨𝐧 #𝐈𝐬𝐥𝐚𝐦𝐢𝐜𝐄𝐝𝐮𝐜𝐚𝐭𝐢𝐨𝐧 🤍📖🕌

12/06/2026

School for Qur'anic Memorization Training
Tadrib Competition

Bashir Lawal fans Abdurrashid M. Sh*tu

12/06/2026

School for Qur'anic Memorization
Tadrib Competition
#

Photos from School for Qur'anic Memorization Training's post 11/06/2026

╔════❖•🕌📖•❖════╗
✨ DAY 6 – CIGABA DA GUDANAR DA TADRIBUL QUR'AN ✨
╚════❖•🕌📖•❖════╝
🕋 ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WA BARAKATUHU 🕋
🌹 Alhamdulillah, cikin ikon Allah Maɗaukakin Sarki, an shiga Rana ta Shida (Day 6) na gudanar da Tadribul Qur'an a SCHOOL FOR QUR'ANIC MEMORIZATION TRAINING.

📖 Muna ci gaba da horas da ɗalibai kan: ✅ Inganta karatun Al-Qur'ani
✅ Gyaran Tajwidi
✅ Ƙarfafa Haddar Al-Qur'ani
✅ Koyarwa cikin tsari da kulawa

🤲 Muna roƙon Allah (SWT) Ya sanya albarka a wannan karatu, Ya ƙara mana ilimi mai anfani, Ya ba ɗalibai fahimta da sauƙin haddar Al-Qur'ani.
💎 “The best among you are those who learn the Qur'an and teach it.”

— Prophet Muhammad (SAW)
━━━━━━━━━━━━━━━ 🏫 SCHOOL FOR QUR'ANIC MEMORIZATION TRAINING
📅 Day 6
📖 Tadribul Qur'an Program ━━━━━━━━━━━━━━━



🕌📖✨🤍

Want your school to be the top-listed School/college in Jos?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Jos

Category

Telephone

Website

Address


Unguwar Rimi
Jos