Institute For Practising Islamic Teachings -Darun Nadwah

Institute For Practising Islamic Teachings -Darun Nadwah

Share

education is for all

Photos from Institute For Practising Islamic Teachings -Darun Nadwah's post 11/01/2022

TEN (10) GOLDEN SECRETS OF MARRIAGE:

✍️Aliyu Nuhu

TO THOSE WHO ARE MARRIED AND/OR ARE PREPARING TO GET MARRIED SOON

1. EVERYONE YOU MARRY HAS A WEAKNESS

Only God has no weakness. Every rose flower has its own thorn. If you focus too much on your spouse's weakness, you can't get the best out of his/her strength.

2. EVERYONE YOU MARRY HAS A DARK HISTORY

No one is an Angel, therefore, avoid digging one's past. What matters is the present life of your partner. Old things are passed away,try to forgive and forget. The past can't be changed. So Focus on the present and the future!

3. EVERY MARRIAGE HAS IT'S OWN CHALLENGES

Marriage is not bed of roses. Every shinning marriage has gone through its own test of hot and excruciating fire. True love is proven in time of challenge. Fight for your marriage! Make up your mind to stay with your spouse in time of needs. Remember this is the vow you made on your wedding day!

4. EVERY MARRIAGE HAS DIFFERENT LEVELS OF SUCCESS

Don't compare your marriage with anyone! We can never be equal, some will be far in front and others far behind. To avoid marriage stresses, be patient, work hard and with time, your marriage dreams shall come true.

5. TO MARRY IS TO DECLARE A WAR

When you marry, you must declare a war against enemies of marriage. Some of the enemies of marriage are: Ignorance, Prayerlessness, Unforgiveness, Adultery, Third Party Influence, Stinginess, Stubbornness, Lack Of Love, Rudeness, Wife battery, Laziness, Divorce etc. Be ready to fight to maintain your marriage zone.

6. THERE IS NO PERFECT MARRIAGE

There is no ready made marriage anywhere. Marriage is hard work, volunteer yourself and perfect it daily. Marriage is like a CAR with Gear oil, gear box, back axles and If these parts are not properly maintained, the car will brake down somewhere along the road and expose the occupant to unhealthy circumstances. - Many of us are careless about our marriages

7. GOD CANNOT GIVE YOU THE COMPLETE PERSON YOU DESIRE

He (God) gives you, him or her in the form of raw materials in order for you to mould what you desire. You may desire a woman who can pray for 1 hour but your wife can only pray for 30 minutes. With your love, prayer and encouragement, she can improve.

8. TO MARRY IS TO TAKE A RISK

You cannot predict what will happen after marriage, as situation may change, so, leave a room for adjustment. Pregnancy may not come in the next 4 years. You may get marred to her because she's slim but she becomes 100% fatter after a child. He may lose his beautiful job for years that you have to take the financial responsibility of the family until he gets a new job. But with God by your side, you will smile at last.

9. MARRIAGE IS NOT A CONTRACT, IT IS PERMANENT

Marriage needs total commitment, love is the glue that makes a couple stick together. Divorce starts in the mind. Never think of divorce! Never threaten your spouse with divorce. Choose to remain married! God hates divorce

10. EVERY MARRIAGE HAS A PRICE TO PAY

Marriage is like a bank account. It is the money you deposit into your bank account that you can withdraw. If you don't deposit love, peace and care into your marriage, you are not a candidate of a blissful home. There is no free love in marriage, You cannot love without giving and sacrificing.

May God Give us The Grace And Wisdom To Build A Heaven on Earth Marriage.

Photos from Institute For Practising Islamic Teachings -Darun Nadwah's post 11/01/2022

Debate

11/01/2022

Allah ya gafarta ma Sheikh

11/01/2022
Photos from Institute For Practising Islamic Teachings -Darun Nadwah's post 11/01/2022

At-tatbiq Central Mosque Shanono Rigasa lokacin ake gabatar da Muqala tsakanin dalibai maza da mata.

16/12/2021

MUHADARA
MUHADARA
MUHADARA
MUNA FARIN CIKIN GAYYATAR YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI ZUWA WAJEN MUHADARA DOMIN TAYA DANUWA

MALAM ABUBAKAR SULAIMAN (ABU ABDALLAH)
MURNAR AURE WANDA ZAI GUDANA KAMAR HAKA:

RANAR JUMAA
12/05/1443 (17/12/2021)
I
LOKACI TSAKANIN MAGRIBA
WURI MASALLACIN JUMA A NA ATTATBIQ
TURAKI ROAD SHANONO RIGASA
MALAMAN DA ZASU GABATAR

SHEIKH AMINU SAUTUS SUNNAH

SHEIKH MUSA YUNUS TAHIR

SHEIKH UMAR MIKAIL(SAYYIDINA UMARU)

SHEIKH IBRAHIM TAYYIB

ALLAH YA BADA IKON HALARTA AMEEN.

31/03/2021

SAHABBAN MANZON ALLAH (SAW) KAMAR YADDA HADISAI S**A BAYYANA SU

MUKALAR DA
MUHAMMAD MANSUR IBRAHIM, PhD
Ya Gabatar

A Taron Kara wa Juna Sani A Kan Gudunmawar Sahabban Manzon Allah Wajen Kafuwar Daular Musulunci ta Farko

Dutse 30-31/Maris 2013M (18-19 J. Ula 1434H)

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Gabatarwa
Kowace al'umma tana tinqaho ne da tarihinta. Kuma magabatan kowace al'umma ana kallon su a matsayin abin girmamawa da darajantawa wadanda kan zama abin koyi ga na baya. Al'ummar musulmi ba a bar ta a baya ba wajen sanin matsayin magabata kamar yadda karantarwar Alqur'ani ta nuna.
((والذين جاؤوا من بعدهم..))
((ويستغفرون للذين آمنوا..))
Sahabban manzon Allah (SAW) su ne almajiransa da s**a rayu da shi, s**a sha daga mavuvvugar ilminsa mai tarin yawa da albarka. Haka kuma su ne waxanda duk tsawon rayuwarsa yake tare da su, kuma duk wata nasara da Allah ya ba shi a cikin rayuwarsa to, su ne abokan cin nasarar nan masu farin ciki da ita. Haka kuma duk wata matsala da ya gamu da ita to, su ne abokan juyayi da jin damuwa a kanta. Kamar yadda buwayayyen sarki Allah ya ce:
((هو الذي أيدك بنصره وبالمؤمنين * وألف بين قلوبهم..))
Sahabbai su ne surukan manzon Allah (SAW) waxanda ya auri 'ya'yansu kuma ya aura masu nasa 'ya'ya. Su ne kuma wadanda s**a ba da rayuwarsu da dukiyarsu da mutuncinsu saboda kariyarsa da ci gaban addininsa har sai da s**a cimma babban abin fata shine yardar Allah madaukakin sarki kamar yadda Alqur'ani ya shelanta haka. Allah Tabaraka Wa Ta'ala ya ce:
((لكن الرسول والذين آمنوا معه جاهدوا بأموالهم وأنفسهم في سبيل الله، وأولئك لهم الخيرات وأولئك هم ..))
Kuma ya ce:
((والسابقون الأولون من المهاجرين والأنصر والذين اتبعوهم بإحسان رضي الله عنهم ورضوا عنه..))
Maqasudin wannan mukala shine fito da matsayin sahabban manzon Allah (SAW) da fifikon su a kan sauran musulmi kamar yadda manzon Allah din da kansa ya bayyana su. Haka kuma mukalar zata tattauna a kan wasu hadisai da ake yi wa kuskuren fahimta a dauke su a matsayin s**a da zargi ga sahabbai, da kuma wasu hadisai da masu son zuciya s**a qirqiro don bata hasken rayuwar waxannan bayin Allah nagartattu s**a jingina su manzon Allah (SAW). Zata kuma yi ishara zuwa ga yadda mabiyan Sunnah suke auna abinda aka bijiro na tarihi wanda ya ci karo da irin waxannan tabbatattun hadissai gami da ayoyin Alqur'ani da kyakkyawar natijar da suke fita da ita wadda ke lamunce musu samun tsira.
Ba dukkan hadisan da s**a zo a kansu ne wannan mukala zata yi magana ba sai dai zamu fito da manyan manufofin da hadisan s**a kunsa ne ta hanyar bada misali.

Ingantattun Hadisan da S**a yi Magana A Kan Sahabbai
1. Fifikon zamaninsu
عن عبد الله بن مسعود رضي الله عنه قال: سئل رسول الله صلى الله عليه وسلم: أي الناس خير؟ قال: ((قرني، ثم الذين يلونهم ثم الذين يلونهم، ثم الذين يلونهم، ثم يجيء قوم تبدر شهادة أحدهم يمينه وتبدر يمينه شهادته)) أخرجه البخاري في الشهادات باب لا يشهد على شهادة جور إذا شهد (2652)، ومسلم في فضائل الصحابة باب فضل الصحابة ثم الذين يلونهم (2533).
Dalilin fifikonsu shine, sun yi imani tun da wuri, sun samu rigaye. Sun taimaki manzon Allah a lokacin tsanani da bukata. Sun kuma yaxa addini, sun samu ladar duk wanda yake bayan su. Duba At- Tamhid na Ibn Abdil Barr (20/251) da Faidh Al Qadeer na Munawee (3/478).

2. Sahabbai su ne garkuwar wannan al'umma
ففي صحيح مسلم من طريق سعيد بن أبي بردة ابن أبي موسى عن أبي بردة عن أبيه قال : صلينا المغرب مع رسول الله – صلى الله عليه وسلم – ثم قلنا : لو جلسنا حتى نصلي معه العشاء ، قال : فجلسنا فخرج علينا فقال : "ما زلتم ههنا ؟" قلنا : يا رسول الله ، صلينا معك المغرب . ثم قلنا ، نجلس حتى نصلي معك العشاء ،قال : "أحسنتم أو أصبتم" قال فرفع رأسه إلى السماء وكان كثيراً مما يرفع رأسه إلى السماء فقال "النجوم أمنة للسماء . فإذا ذهبت النجوم أتى السماء ما توعد . وأنا أمنة لصحابي فإذا ذهبت أتى أصحابي ما يوعدون وأصحابي أمنة لأمتي ، فإذا ذهب أصحابي أتى لأصحابي متى ما يوعدون" أخرجه مسلم في كتاب فضائل الصحابة باب بيان أن بقاء النبي صلى الله عليه وسلم (2531).
Fassarar wannan shine, kamar yadda taurari suke garkuwa ga wargajewar sama da faruwar tashin qiyama, idan sun gushe alqiyama zata faru. Haka shi kuma Annabi (SAW) garkuwa ne daga rabuwar kan sahabbai da aukuwar fitinar yaqin basasa a tsakaninsu. Amma bayan wucewar sa hakan ta faru. Su kuma sahabbai garkuwa ne ga al'ummar musulmi daga fantsama a cikin bidi'ah da lalata hasken addini. Amma bayan wucewar su sai wannan ya faru. Duba sharhin Imam An Nawawi a kan Sahih Muslim (16/83).
Muna iya lura cewa, hadisin ya bada cikakkiyar sheda ga tsarkin addininsu da kyawon aqidarsu, amma bai mayar da su ma'asumai ba. Wannan kuwa ya zo daidai da ayoyin Alqur'ani masu yawa da s**a yaba ma imaninsu da hijirarsu da jihadinsu da s**a yi saboda neman yardar Allah.

3. Darajar Mujahidan Badar:
عن رفاعة بن رافع الزرقي عن أبيه ـ وكان أبوه من أهل بدر ـ قال: جاء جبريل إلى النبي صلى الله عليه وسلم فقال: ما تعدون أهل بدر فيكم؟ قال: "من أفضل المسلمين" ـ أو كلمة نحوها ـ قال: وكذلك من شهد بدراً من الملائكة". أخرجه البخاري في كتاب المغازي باب: شهود الملائكة بدراً (3992)، وابن ماجة في المقدمة باب فضل أهل بدر (160).

وعن جابر رضي الله عنه أن عبداً لحاطب جاء رسول الله صلى الله عليه وسلم يشكو حاطباً فقال: يا رسول الله ليدخلن حاطب النار، فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم: "كذبت، لا يدخلها، فإنه شهد بدراً والحديبية" أخرجه مسلم في كتاب فضائل الصحابة باب: من فضائل أهل بدر رضي الله عنهم (2495).
Wannan gafara da Allah ya yi wa mujahidan Badar ta shafi hukuncinsu a alqiyama ne. Amma a nan duniya ana yanke masu hukunci idan sun yi laifi kamar kowa. Kamar yadda manzon Allah (SAW) ya tsayar da haddi a kan Misxah bin Uthatha a lokacin ya sa bakinsa cikin qazafin da aka yi wa uwar muminai. Haka shi ma sayyidina Umar (RA) ya tsayar da haddin shan giya a kan Qudamah bin Maz'un. Duka su biyun na daga cikin mujahidan Badar da Allah ya gafarta ma.

4. Matsayin waxanda s**a halarci yaqin Uhud
عن ابن عباس رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: "لما أصيب إخوانكم بأحد جعل الله عز وجل أرواحهم في أجواف طير خضر ترد أنهار الجنة تأكل من ثمارها، وتأوي إلى قناديل من ذهب في ظل العرش، فلما وجدوا طيب مشربهم ومأكلهم وحسن منقلبهم قالوا: يا ليت إخواننا يعلمون بما صنع الله لنا لئلا يزهدوا في الجهاد ولا ينكلوا عن الحرب فقال الله عز وجل: أنا أبلغهم عنكم"، فأنزل الله عز وجل هؤلاء الآيات على رسوله: {وَلاَ تَحْسَبَنَّ ٱلَّذِينَ قُتِلُواْ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ أَمْوٰتاً بَلْ أَحْيَاء عِندَ رَبّهِمْ يُرْزَقُونَ} [آل عمران:169]. أخرجه أبو داود في كتاب الجهاد باب: في فضل الشهادة (2520)، وأخرجه الإمام أحمد في مسنده برقم (2384)، والحديث حسنه الألباني في صحيح سنن أبي داود برقم (2199) (2/479).

5. Darajar waxanda s**a yi mubaya'a a Hudaibiyyah
عن جابر بن عبد الله رضي الله عنهما قال: قال لنا رسول الله صلى الله عليه وسلم يوم الحديبية: "خير أهل الأرض" وكنا ألفاً وأربعمائة، ولو كنت أبصر لأريتكم موضع الشجرة. أخرجه البخاري في كتاب المغازي باب: غزوة الحديبية (4155)، ومسلم في كتاب الإمارة باب: استحباب مبايعة الإمام الجيش (4155).
وعن جابر بن عبد الله رضي الله عنهما قال: أخبرتني أم مبشر: أنها سمعت النبي صلى الله عليه وسلم يقول عند حفصة: "لا يدخل النار إن شاء الله من أصحاب الشجرة أحد الذين بايعوا تحتها" قالت: بلى يا رسول الله، فانتهرها فقالت حفصة: {وَإِن مِّنكُمْ إِلاَّ وَارِدُهَا} فقال النبي صلى الله عليه وسلم: ((قد قال الله عز وجل: {ثُمَّ نُنَجّى ٱلَّذِينَ ٱتَّقَواْ وَّنَذَرُ ٱلظَّـٰلِمِينَ فِيهَا جِثِيّاً} [مريم:72])) أخرجه مسلم في كتاب فضائل الصحابة باب: من فضائل أصحاب الشجرة وأهل بيعة الرضوان (2496).

6. Son Sahabbai Wajibi ne:
عن عبد الله بن مغفل المزني قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: "الله الله في أصحابي، لا تتخذوهم غرضاً بعدي، فمن أحبهم فبحبي أحبهم، ومن أبغضهم فببغضي أبغضهم، ومن آذاهم فقد آذاني، ومن آذاني فقد آذى الله، ومن آذى الله يوشك أن يأخذه" أخرجه الترمذي في كتاب المناقب باب: فيمن سب أصحاب النبي صلى الله عليه وسلم (3862) والحديث ضعفه الألباني في ضعيف سنن الترمذي برقم (808) وقال عنه الترمذي: هذا حديث حسن غريب لا نعرفه إلا من هذا الوجه.

7. Son "Ansar" yana cikin Imani:
عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: "لا يبغض الأنصار رجل يؤمن بالله واليوم الآخر" أخرجه البخاري في كتاب المناقب باب: حب الأنصار (3783)، وأخرجه مسلم في كتاب الإيمان باب الدليل على أن حب الأنصار وعلي رضي الله عنه (75).
وعن عدي بن ثابت قال: سمعت البراء يحدث عن النبي صلى الله عليه وسلم أنه قال في الأنصار: "لا يحبهم إلا مؤمن، ولا يبغضهم إلا منافق، من أحبهم أحبه الله، ومن
أبغضهم أبغضه الله" أخرجه مسلم في كتاب الإيمان باب: الدليل على أن حب الأنصار وعلي رضي الله عنه (76)

8. Wasici da iyalan gidan manzon Allah (SAW)
قول النبي صلى الله عليه وسلم: "أما بعد: ألا أيها الناس، فإنما أنا بشر يوشك أن يأتي رسول ربي فأجيب، وأنا تارك فيكم ثقلين: أولهما كتاب الله فيه الهدى والنور فخذوا بكتاب الله واستمسكوا به" فحث على كتاب الله ورغب فيه ثم قال: "وأهل بيتي، أذكركم الله في أهل بيتي، أذكركم الله في أهل بيتي، أذكركم الله في أهل بيتي" أخرجه مسلم في كتاب فضائل الصحابة باب: فضائل علي بن أبي طالب (2408).
Masu dogon nazari daga vikin ma'abota ilmi sun gano a wannan hadisi cewa, manzon Allah (SAW) yana sane da cewa, tafiyar da sha'anin wannan al'umma a bayansa ba ga iyalansa zai koma ba. Domin da su ne zamu mulki sai ya ce ma su "Ina tunatar da ku Allah game da sahabbaina".
9. Hatsarin cuta masu
عن عبد الله بن مغفل المزني _رضي الله عنه_ قال : قال رسول الله -صلى الله عليه وسلم- "الله الله في أصحابي، الله الله في أصحابي، لا تتخذوهم غرضا بعدي فمن أحبهم فبحبي أحبهم ومن أبغضهم فببغضي أبغضهم ومن آذاهم فقد آذاني ومن آذاني فقد آذى الله تبارك وتعالى ومن آذى الله فيوشك أن يأخذه"
رواه أحمد 5/54 والترمذي (3862) والبيهقي في الشعب 2/191 وقال الترمذي : هذا حديث غريب لا نعرفه إلا من هذا الوجه ا.هـ .

10. Haramcin zagin su
عن أبي هريرة _رضي الله عنه_ قال : قال رسول الله -صلى الله عليه وسلم- "لا تسبوا أصحابي لا تسبوا أصحابي فوالذي نفسي بيده لو أن أحدكم أنفق مثل أحد ذهبا ما أدرك مد أحدهم ولا نصيفه" رواه البخاري (3470 ) ومسلم (2540) واللفظ له .
وعن ابن عباس رضي الله عنهما أن النبي صلى الله عليه وسلم قال: "من سب أصحابي فعليه لعنة الله والملائكة والناس أجمعين" أخرجه الطبراني في الكبير (3/174) وحسنه بمجموع طرقه الألباني في السلسلة الصحيحة (2340).
Sharhin Ibn Taimiyyah a kan waxannan hadissai:
Shehin musulunchi Ibn Taimiyyah yana cewa: "Hadisan nan da ke maganar girman matsayin sahabbai da yaba masu da fifita zamaninsu a kan na bayan su hadisai ne da s**a game duniya (Mutawatirai). Saboda haka yin s**a a kan su yin s**a ne ga Alqur'ani da hadisi. Don haka ne ma mutane (yana nufin malamai) s**a rinka magana a kan kafircin 'yan Shi'ah, bayanin da mun riga mun shinfida shi a wani littafi ba wannan ba". Majmu' Al- Fatawa (4/430).
Akwai kuma hadisai masu tarin yawa da s**a bayyana falalar wasu xaixaiku daga cikin sahabbai da iyalan manzon Allah (SAW) waxanda ba za a samu damar kawo su ba - saboda buqatar taqaitawa - a cikin wannan mukala. Amma a qunshe suke cikin "Kitabul Fadha'il" na cikin Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim da sauran littafan Sunnah.

Shubhohin 'Yan Shi'ah Daga Cikin Hadisai
Addinin Shi'ah shubha ce zallarta. Shi ya sa ba su da aiki sai wahalar da malamai wajen maida masu martani. Haka kuma addinin nasu addini ne marar makama. Zaka gane wannan in kayi la'akari da cewa, duk wata aqidarsu ko fahimtarsu zaka iya warware ta daga cikin littafansu xin kansu. 'Yan Shi'ah s**an yi fatali da hadissan nan duka da muka kawo da ma duk ire-irensu. Hujjarsu a kan wannan ita ce, ai su dai sahabban ne s**a ruwaito hadisan da kansu. Idan kuwa aka bi wannan tafarki nasu - na qin amincewa da sahabbai, duk da yake Allah da kansa ya amince da su - Alqur'ani ma ba zai tsira ba tun da su ne s**a karantar da mu shi. A maimakon haka, 'yan Shi'ah suna amfani da wasu hadissai wajen s**a da tuhuma da suke yi ma sahabban manzon Allah (SAW) cewa, sun yi ridda kuma sun canja addini. Ga yadda hadissan da su ke kafa hujja da su suke:
Na farko: Hadisai Ingantattu
Akwai hadissan da suke ingantattu ne amma ba su nuna zargi ko s**a ga sahabbai, sai dai s**an jirkita ma'anarsu ko su xora su a inda son zuciyarsu ya ga dama. Misalin wannan shi ne:
Hadisin Ridda
An fi sanin wannan hadisi da "Hadith Al- Haudh" kuma ingantaccen hadisi ne wanda babu tantama a game da ingancinsa. Sai dai masu son zuciya sun yi amfani da shi don qarfafa tuhumar da suke yi ma sahabban manzon Allah (SAW) da yin ridda bayan wafatinsa.
Nassin hadisin:
عن سهل بن سعد قال قال النبي صلى الله عليه وسلم: "إني فرطكم على الحوض، من مر علي شرب ومن شرب لم يظمأ أبدا. ليردن علي أقوام أعرفهم ويعرفوني ثم يحال بيني وبينهم". قال أبو حازم: فسمعني النعمان بن أبي عياش فقال هكذا سمعت من سهل؟ فقلت: نعم. فقال اشهد على أبي سعيد الخدري لسمعته وهو يزيد فيها "فأقول: إنهم مني فيقال انك لا تدري ما أحدثوا بعدك، فأقول سحقا سحقا لمن غير بعدي" صحيح البخاري ٦٠٩٧
An karbo daga Abu Hazim daga Sahl bin Sa'ad (RA) ya ce, annabi (SAW) ya ce: "Ni zan riga ku zuwa tafkin (Al-Kauthar). Duk wanda ya same ni a wurin zai sha. Wanda kuwa duk ya sha ba zai sake qishi ba har abada. Kuma lalle wasu jama'a zasu same ni, na san su, sun san ni. Sannan sai a shamakance a tsakani na da su".
Abu Hazim ya ce: Sai Nu'uman bin abi Ayyash ya ji ina faxin hadisin, sai ya ce, haka ka ji shi a wurin Sahl bin Sa'ad (RA)? Sai na ce, eh. Ya ce, ni kuma na sheda cewa na ji shi daga Abu Sa'id Al-khudri (RA) kuma yana qarawa da cewa, "Sai in ce, su suna daga gare ni. Sai a ce min, ai baka san irin abinda s**a farar ba a bayanka. Sai in ce, nesa.. nesa da waxanda s**a canja a bayana".
Wannan hadisi ya tabbata ta hanyar sahabbai da dama kamar Anas (Bukhari 6582, Muslim 2304) da Sahl bin Sa'ad (Bukhari 6585) da Asma'u bint Abibakr (Bukhari 6593, Muslim 2293) da Abdullahi bin Mas'ud (Bukhari 6593) da wasu sahabbai da dama. Kuma ya zo da lafazi iri daban daban, wanda ya tattara lafuzzansa idan yana da tsarkin zuciya zai yi ma sa fahimta mai kyau. Ya kuwa za ayi mai tsarkin zuciya da ya yarda da abinda Allah da manzo ya faxi a kan su cewa, Allah ya yarda da su, kuma ya san tsarkin zukatansu, har ya ce ya bada misalinsu a cikin Taurata da Linjila, kuma ya yaba ma su a kan jihadin da s**a yi da taimakon manzon Allah, sannan ya jinjina ma masu yi masu addu'a da roqon gafara, ya yi allawaddai da munafukai da ke masu izgili, kuma ya ce, da su ne ya qarfafi annabinsa. Ya za ayi wanda ya yarda da wannan ya munana fahimtar irin wannan hadisi?! Tarihi ma ba zai qarfafa maganar riddar sahabbai ba in aka kalli irin jajircewar da s**a yi da sadaukarwa wadda tarihi bai tava ganin irinta ba. Kuma ma da ridda ta bayyana bayan wafatin manzon Allah (SAW) ai sahabban ne s**a yaqi 'yan ridda. Ga dai wasu daga cikin maganganun malamai magadan annabawa masu tsarkin zuciya a kan wannan hadisi:
1. Hadisin ya yi maganar waxanda zasu yi ridda ne, ya kira su sahabbai da ma'anar su mabiyan annabi ne ba almajirai ko sahabban da s**a zauna da shi ba. Kamar yadda ake cewa "As'habu Malik" da "As'habus Shafi'i" da sauran su.
2. Ba wanda ya yi ridda daga cikin sahabban da s**a zauna tare da manzon Allah (SAW). Waxanda s**a yi ridda sune qauyawan da s**a ji labarin musulunci kuma s**a musulunta saboda wasu dalilai, amma basu tava taimaka ma addini ko yin yaqi don kariyar sa ba. Waxannan 'yan kaxan ne kamar yadda lafazin "Usaihabi" wato 'yan sahabbaina yake nunawa. Haka ma akwai ruwayar da ta ce, "Rahxun min as'habi" wanda yake nuna yawansu daga mutane uku ne zuwa goma domin shi kalmar "Rahx" take nunawa.
3. Ko kuma yana nufin su munafukai ne tunda bai san su duka ba kamar yadda Allah ya ce: "Kai ba ka san su ba. Mu ne muka san su". Kuma ai a zahiri su sahabbai ne tunda sun shiga cikin jama'arsa. shi ya sa da aka ce ma manzon Allah (SAW) ya kashe su ya ce, a'a. Ba zan bari mutane su ce Muhammadu yana kashe sahabbansa ba".
4. Wasu malaman na ganin cewa, hadisin yana nuni da 'yan bidi'a da s**a canja addinin Allah daga yadda manzo ya bar shi domin a hadisin yana cewa: "Sai a ce min: ba ka san irin abinda s**a farar ba a bayanka".
5. Wasu malaman na ganin ban da 'yan bidi'a ma akwai yiwuwar masu sabo su shiga ciki. Tunda wannan magana ta nuna zasu shiga wuta amma ba ta nuna zasu dawwama ba.
6. Wasu kuma na da ra'ayin cewa, hadisin na nuni ne zuwa ga Khawarij, waxanda hadisai da dama sun bayyana su da masu ficewa daga addini kamar yadda kibiya ke fita daga dabbar da aka harba.
Duk waxannan maganganu suna tattare a littafin Imam An-Nawawi na sharhin Sahih Muslim (3/136-137).
Shi kuma shehun malamin nan na malikiyyah Al-Hafizh Ibn Abdilbarr yana ganin cewa, duk waxannan da aka faxa zai yiwu a kore su daga shan ruwan tafkin Al-Kauthar tunda yake lafuzzan hadisin suna nuna haka. At- Tamhid (20/262) da kuma At-Tadhkirah na Imam Al-Qurtubi (1/348).
To, amma masu son zuciya sai su kafa hujja da cewa, annabi (SAW) ya ce ya san su. Sai su manta ruwayar da ta faxi cewa ya san su ne da alamomin da ke fuskarsu da hannaye da qafafunsu na hasken alwala.
Nasibawa su kuma sai su kan xora wannan hadisi a kan sayyidina Ali da 'ya'yansa. Ba kuwa yadda zaka iya ba su amsa sai ta hanyar Ahlus-Sunnah. Kuma duk wani yunqurin tuhumar sahabbai da yin ridda idan da zai tabbata a kan su to, ba zai koru ba daga waxannan bayin Allah. ina nufin sayyidina Ali da 'ya'yansa. Allah ya yi mana kariya daga son zuciya.

Misali na biyu: Hadisin Abdullahi bn Amr wanda Muslim ya ruwaito cewa:
"إذا فتحت عليكم خزائن فارس والروم أي قوم أنتم؟" فقال عبد الرحمن بن عوف: كما أمرنا الله تعالى. فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم: "كلا، بل تتنافسون ثم تتدابرون ثم تتباغضون ثم تنطلقون إلى مساكن المهاجرين فتحملون بعضهم على رقاب بعض". صحيح مسلم رقم ٢٩٦٢
Wannan hadisi kamar yadda muka gani ya tabbatar da cewa, masu laifin ba muhajirai ne ba. Haka kuma tarihi ya tabbatar ba Ansarai ne ba. Domin babu inda Ansar s**a haxa muhajirai faxa. Su wane ne kenan? Su ne 'yan baya, fitinannu, tsinannu irin su Ashtar An-Nakha'i waxanda s**a yi wa sayyidina Usman (RA) juyin mulki kuma s**a kashe shi, s**a haddasa rikici mai yawa a tsakanin al'umma.

Misali na uku: Ruwayar da ta zo daga Anas bn Malik (RA) inda yake cewa:
لا أعرف شيئا مما أدركت إلا هذه الصلاة وقد ضيعت. رواه البخاري رقم ٥٣٠
Sai masu son zuciya - 'Yan Shi'ah - suna kafa hujja da wannan magana cewa, sahabbai sun canja komai na addini! Anas (RA) kuwa ya faxi wannan maganar ne a zamanin sarki Hajjaj wanda aka san shi da jinkirta sallah har lokacinta ya yi nisa. A lokacin kuwa sahabbai na da qaranci qwarai. kuma a kan haka ne Ibnu Umar (RA) ya daina bin sa sallah. Wasu kuma s**a rinqa yin sallarsu a cikin lokaci, idan ya tayar da tasa sallar sai su bi shi a matsayin nafila don kada su raba kan jama'a kuma su janyo ma kansu ta'addancinsa. Don haka ba inda wannan magana ta Anas ta nuna cewa sahabbai sun tozarta sallah.
Abin ban mamaki ma shine yadda a wani lokaci zaka samu nassoshi da suke nuna alherin sahabbai sai - da gangan - a juya su a mayar da su abin s**a a gare su. Misalin wannan shine hadisin Abu Sa'id Al-Khudri (RA) da ke cikin Bukhari da Muslim:
عن أبي سعيد الخدري رضي الله عنه قال: (كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يخرج يوم الفطر والأضحى إلى المصلى، فأول شيء يبدأ به الصلاة ثم ينصرف فيقوم مقابل الناس - والناس جلوس على صفوفهم - فيعظهم ويوصيهم ويأمرهم، فإن كان يريد أن يقطع بعثاً قطعه أو يأمر بشيء أمر به ثم ينصرف. قال أبو سعيد: فلم يزل الناس على ذلك حتى خرجت مع مروان - وهو أمير المدينة - في أضحى أو فطر، فلما أتينا المصلى إذا منبر بناه كثير بن الصلت، فإذا مروان يريد أن يرتقيه قبل أن يصلي فجبذتُ بثوبه فجبذني فارتفع فخطب قبل الصلاة فقلت له: غيّرتم والله، قال: أبا سعيد قد ذهب ما تعلم، فقلت: ما أعلم والله خير مما لا أعلم، فقال: إن الناس لم يكونوا يجلسون لنا بعد الصلاة فجعلتها قبل الصلاة) أخرجه البخاري (956) واللفظ له ومسلم (889).
Ga shi qarara a cikin hadisin sahabbai suna kariyar sunnar manzon Allah (SAW) daga canjin da 'yan baya s**a yi, amma sai ake kawo hadisin a matsayin hujjar cewa, sun canja ma manzon Allah sunnarsa. Shi kansa Marwan - duk da yake ba sahabi ba ne - ya nuna ijtihadi ne ya yi domin mutane su saurari huxuba kar su watse, ba ya yi haka ba ne kawai don yana son ya canja sunnah.

Kashi na biyu: Hadisai Marasa Inganci da kuma qagaggu waxanda aka kitsa su musamman don tabbatar da waccan aqida ta yin s**a ga almijiran fiyayyen halitta. Idan muna maganar tarihi wannan fage ba a ko magana. Domin abinda kundin tarihi ya qunsa na labaran qarya da shaci-faxi waxanda aka yi su da wannan manufa ba wanda ya san iyakarsu sai Rabbus-samawati. Amma hadissan da aka jingina ma manzon Allah bisa qarya a kan xaixaikun sahabbai da kuma ilahirinsu to, waxannan malamai sun tona asirinsu. A nan dai zamu bada 'yan misalai ne a kan abinda s**a faxa a kan wasu xaixaikun sahabbai:
1. Hadisin
"إذا رأيتم معاوية على منبري فاقتلوه"
An bincika littafan musulunci gaba xaya ba a samu wannan hadisi ba. Don haka ne ma Ibnul Jauzi ya sa shi a cikin "kundin hadisan qarya" AL-MAUDHU'AT (2/25).
Akwai xan uwan wannan hadisi da yake cewa:
عن عبد الله بن عمر قال: أتيت النبي صلى الله عليه وسلم فسمعته يقول: "يطلع عليكم رجل يموت على غير سنتي" فطلع معاوية.
Da na ukunsu wanda yake cewa:
قام النبي صلى الله عليه وسلم خطيبا فأخذ معاوية بيد ابنه يزيد وخرج ولم يسمع الخطبة، فقال النبي صلى الله عليه وسلم: "لعن الله القائد والمقود".
Ga dukkan alamu wanda ya qaga wannan na uku ya haxa qarya da rafkanwa. Domin kuwa tarihi ya sheda cewa, ba a haifi Yazid ba a zamanin manzon Allah (SAW) ko zamanin Abubakar ko Umar (RA). An haife shi ne a zamanin sarkin musulmi Usman (RA). To, ya aka yi manzon Allah (SAW) ya gan shi har ya la'ance shi alhalin ba a ko haife shi ba?!
Malaman tarihi sun haxu a kan kawo wasicin da manzon Allah (SAW) ya yi wa sayyidina Mu'awiyah cewa, idan ka jivinci wani al'amari na wannan al'umma to, ka ji tsoron Allah kuma ka yi adalci. Wanda Mu'awiyah ya ce, tun daga ranar nake xammahar yin sarauta.
Sau da yawa rashin sani kan sa wasu daukar cewa, samun irin waxannan hadisan a cikin littafan Sunnah shi kaxai ya isa ya tabbatar da ingancinsu. Da yawa ma mabiyan Shi'ah kan yi tutiya da wannan cewa ai ga hadisan nan ma a cikin littafanku. Alhali kuwa a duk inda aka samu ruwaya wajibi ne a xora ta a ma'aunin ilmi don tabbatar da sahihancinta ko rauninta. Daga nan ne ma za a iya gano ko idan zuqi ta mallau ce. Sai fa idan an same ta a xaya daga cikin littafan zaqaquran malamai waxanda s**a sharxanta inganci kamar Bukhari da Muslim.

Qa'idar da Ahlus-sunnah suke bi a game da ayoyi da hadisai da ake ganin kamar sun kunshi s**a ga Sahabbai:
1. Dole ne mu mayar da duk abinda ya rikitar da mu zuwa ga wanda ba shi da rikici. Alqur'ani a cike yake da yabon sahabban manzon Allah. Haka ma ingantattun hadisai. A cikinsu har da waxanda suke ba su shedar zama yardaddu a wurin Allah, masu gaskiyar imani da yin jihadi saboda Allah, da kuma tabbatar da cewa su 'yan aljanna ne.
2. Duk nassin da ya saba ma wannan idan aka bi diddigi za a tarar bai inganta ba. Ko kuma ya gamu da sauyi da canja magana zuwa inda ba a nufe ta ba. Ilahirin irin waxannan ruwayoyin na Abu Mikhnaf da Hisham Al-Kalbi ne da sauran maqaryata.
3. Idan kuwa ya inganta bai wuce wani zunubi ne da wani ko wasu daga cikin sahabbai s**a yi, tunda yake su ba ma'asumai ba ne.
4. Galibin zunubi idan ya zo daga irin waxannan zavavvun bayin Allah bai wuce an yi shi ne bisa ga kuskure ko ta'awili ko ijtihadin da Allah yake uzuri gare shi.
5. Umurnin da shari'a ta yi na kyautata ma kowane musulmi zato, da rashin shiga cikin rigar mutuncinsa na wajabta a tantance tarihin duk da yake da alaqa da wasu magabatan musulmi ballantana sahabbai.
6. Zunubi ba shi hana zaman mutum xan aljanna. kamar yadda ba shi wajabta zargi ga irin waxannan mutane bale zagi. Saboda akwai yiwuwar wanda ya yi shi daga bisani ya yi nadama ya koma ma Allah ta hanyar tuba, ko kuma tarin ladarsa ya shafe zunubin, ko an jarabce shi da wata musiba a nan duniya mai goge zunubbai, ko ya samu addu'ar muminai daga cikin mutane ko mala'iku - ko da a bayan mutuwarsa - wadda ta kankare zunubinsa, ko ya yi dace da ceton manzon Allah (SAW) ko dai duk wani dalilin da Allah zai kuvutar da shi daga hatsarin zunubin a cikin rahamarsa.

Nadewa
An umurci musulmi da ya zama mai kyautata addu'a ga waxanda s**a riga shi imani. Kuma ya nemi Allah kariya daga samun wani qulli a zuciyarsa na qiyayya da jin zafi ga muminai. A cikin waxanda s**a riga mu yin imani babu kamar sahabban manzon Allah (SAW) su da wannan addini ya kafu ta hannunsu. Kuma bisa ga umurnin da Allah ya xora ma manzonsa na yin tarbiyyah a gare su, manzo ya yi iyakar qoqarinsa ya kuma ci nasara matuqa ta hanyar sauya rayuwarsu daga shirka zuwa tauhidi, daga jahiliyyah zuwa musulunci. Hadisan manzon Allah (SAW) a cike suke da yabawa a kan waxannan tsarkakun bayi kamar yadda Alqur'ani yake a cike da yabon su.

Taliqin Dr. Abubakar Birnin Kudu (Shugaban zama):
Duk wanda ya samu matsala a kan fahimtar matsayin sahabbai to, zai samu gurguwar fahimta ga addininsa.

26/03/2021

Hikimar Aure:
Manufar Musulunci Ga Aure:

Yana daga cikin hikimar Aure a bautawa Allah kuma a hada kai, a kulla dangan taka.

Kayi Aure ka bautawa Allah don kabi umarnin Allah, kuma kabi umarnin Manzon Allah S.A.W

Kuma a lokaci guda ka shimfida gadar kauna da fahimtar juna da son juna tsakaninka da gidan da kayo Aure, da! bakusan juna ba, baku da alaka bakwa ziyartar juna.

Sana diyar aure sai kaga suna ziyartar idanku idan wani abu mai dadi ko marar dadi ya faru, kaima danginka suna ziyartarsu

Auran ya kulla dangantaka kuma daman wannan shine bukatar Musulunci ga Aure.

Nagegime
Director Media of
Sheik Prof.Pakistan
March 26, 2021

18/03/2021

Gaskiya Mai Daci
✍ Engr. Mustapha Habu Ringim
Founder Engausa Global Tech. Hub
18/03/2021

Rashin iya ingantacciyar sana’ar hannu mai dorewa “technical skills” ne ke kora yawancin mutanen arewa zuwa kudu. Kwarewa da sana’oin hannu ke janyo yawancin mutan kudu zuwa arewacin Nigeria. Ko kuna da ja ??????

Idan kaje kudu duk wani dan menial job ko unskillful labor to dan arewa ne. Mabarata a kudu yawanci ÿan arewa ne. Idan kuma ka zo arewa yawancin masu skillful labor ÿan kudu ne. Saboda shi kwaikwayon menial work babu wahala, kowa ma ya iya, shine yasa ÿan kudu s**a mayar da hankali wajen koyon “ high tech skills” wanda ba kowa ke da kwakwalwar koyo ba, kuma Idan ma ka koya to ba kowa ke da haqurin dagewa har sai ya kware ba. Idan kuma ka kware ba kowa ke da haqurin dogewa kan sana’ar har ya raineta ta girma ba.

MAFITA :
1. Sai mun wayar da kan matasa da iyayen yara kan mahimmancin sana’oin hannu na zamani.
2. Kuma mu yi yunkurin bude guraren koyon sana’oin hannun kamar yadda muke da qoqarin bude private schools.
3. Mu kuma daina raina masu qaramar sana’a. Mu riqa girmama mutum a kan sana’ar sa, domin idan babu mai wannan qaramar sana’ar to sai al’umma ta shiga uku.
4. Mu riqa baiwa masu sana’oin hannu haqqin su, domin kada su gudu wasu garuruwan da akafi basu haqqin su barmu da baragurbin cikin su suyi ta kwaba mana muna sha hakanan kuma babu yadda za muyi.
5. Mu riqa bibiyar yaran mu muna gano baiwar da Allah Ya yi masu domin dora su akan turbar da tafi dacewa da rayuwar su.
6. Kuma sai mun fifita aiki da fahimtar ilimi, da hikima, sama da kwalin certificate.
7. Sai mun mayar da hankali kan tarbiyyar yaran mu sama da yawan dukiyar da zamu tara musu, sama da duk wani shagali da shagalgalewa.

Want your school to be the top-listed School/college in Kaduna?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Telephone

Website

Address


Kaduna